Dakaru masu sanye da kayan sarki na RSF da ke faɗa da sojojin Sudan sun bayyana amincewa da yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta ta sa’a 24, fara wa da misalin karfe 6 na yamma.
Cikin wata sanarwa da dakarun suka wallafa a shafinta na Twitter, ta ce “Mun amince da kudurin tsagaita buɗe wuta, kuma muna fatan sauran ɓangarorin za su bi yarjejeniyar da aka cimma,” in ji kungiyar
Sai dai babu tabbacin cewa ko sojojin Sudan sun amince da tsagaita buɗe wutan.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Ɓangarorin biyu sun ce za su mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta ta sa’o’i 24 a ranar Talata.
Ana dai ci gaba da gwabza kazamin faɗa a ƙasar ta Sudan, musamman a kusa da hedkwatar sojojin da ke tsakiyar birnin Khartoum.
PRNigeria hausa











