Home Labarai Sojojin Nijeriya sun hallaka ‘yan bindiga 36 tare da kwato mutane 140...

Sojojin Nijeriya sun hallaka ‘yan bindiga 36 tare da kwato mutane 140 – DHQ

Shalkwatar rundunar sojin Nijeriya tace cikin makwanni 2 dakarunta sun sami nasarar kame ‘yan ta’adda 137 tare da hallaka’ 36 a fadin kasar.

Haka Kuma cikin makwanni biyun ta sami nasarar ceto mutane 140 daga hannun ‘yan bindigar.

Daraktan sashen yada labaran shalkwatar Manjo Janar Edward Buba, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwar mako – mako da ya fita a birnin tarayya Abuja.

Yace a yayin atisayen dakarun sun kama’ yan bindiga 3, masu garkuwa da mutane 2, sai wadanda ake hadin baki da su mutum 6 sai kuma barin danyen mai su 15 inda suka samu kudi har naira 3,177,650.00.

Janar Buba yace maza da mata a a cikin dakarun sojin Nijeriya sun shirya yaki da dukkan aikin bata gari.

“a shirye muke mu yake su, ya zama waji mu kakkabe su daga cikin mu.”

Yace a cikin makwanni dakarun sun sami nasarar kwato makamai 37 da alburusai 370, bindiga kirar ak47 guda 16, bindiga kirar pump action guda 6, kirar dane guda sai kuma karamar bindiga kirar gida 2 da dai sauran muggan makamai.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp