Home DUNIYA ECOWAS ta bukaci AU da ta amince da kudirorin da ta dauka...

ECOWAS ta bukaci AU da ta amince da kudirorin da ta dauka kan Nijar

Kungiyar Kasashen Yammacin Afrika ta ECOWAS ta umarci rundunarta da ke cikin shirin-ko-ta-kwana da ta maido da kundin tsarin mulki a Jamhuriyar Nijar.

Shugaban gudanarwar ECOWAS Omar Alie Touray ya bayyana haka a lokacin da yake karanta kudirorin da kungiyar ta dauka game da juyin mulkin Nijar a wani taro da ya gudana birnin Abuja na Najeriya a wannan Alhamis.

ECOWAS ta bayyana cewa, ta dauki matsayar ce bayan ta nazarci rahoto da kuma shawarwarin da Kwamitin Hafsosshin Tsaronta ya bayar, tana mai korafin cewa, daukacin hanyoyin diflomasiyar da ta bi don warware rikicin siyasar kasar sun ci-tura sakamakon yadda sojojin suka yi juyin mulki suka ki mutunta umarnin da aka ba su.

ECOWAS ta bai wa sojojin na Nijar wa’adin ranar 6 ga wannan wata na Agusta da su mayar da shugaba Mohamed Bazoum kan kujerarsa ta shugaban kasa, amma suka ki mutunta wannan umarni.

Yanzu haka ECOWAS ta jaddada matsayarta ta yin Allah-wadai da juyin mulkin gami da ci gaba da tsare shugaba Bazoum da iyalansa da wasu jami’an gwamnatinsa.

Kungiyar ta kasashen yammacin Afrika ta sanar da tsaurara matakan rufe kan iyakokin Nijar da haramta tafiye-tafiye da daskarar da kadarorin wadanda ke da hannu a juyin mulkin bayan ta gaza magance rikicin kasar ta hanyar laluma.

A bangare guda, ECOWAS ta bukaci Kungiyar AU da ta amince da daukacin kudirorin da ta dauka a dalilin halin da ake ciki a Jamhuriyar Nijar.

Har ila yau, ECOWAS ta yi kira ga kasashen duniya aminanta da Majalisar Dinkin Duniya da su mara mata baya domin samun natija ta gaggawa dangane da maido da kundin tsarin mulki a Nijar.

Kawo yanzu dai, sojojin da suka yi juyin mulkin na Nijar ba su nuna wata alamar shiga tattaunawar fahimtar juna da ECOWAS ba duk kuwa da tarin takunkuman da aka malkaya musu baya ga barazanar daukar matakin sojin da aka yi musu.

PRNigeria hausa

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp