Home Labarai NASSI Da BOI Sun Sanya Hannu Akan Yarjejeniyar Bawa Ƙananan Masana’antu Rancen...

NASSI Da BOI Sun Sanya Hannu Akan Yarjejeniyar Bawa Ƙananan Masana’antu Rancen Bilyan 75

Ƙungiyar masu ƙanana da matsakaitan Masana’antu ta Najeriya, wato Nigeria Association of Small Scale Industrialists (NASSI), ta sanya hannu akan wata yarjejeniya da Bankin Masana’antu wato Bank of Industry, wadda ta sahale a bawa Mambobin ƙungiyar rancen naira Bilyan 75.

Shugaban NASSI na ƙasa Chief Dakta Solomon Daniel Vonfa ne ya sanya hannu akan takardar yarjejeniya, a inda shi kuma Manajan Daraktan Bankin Dakta Olasupo Olusi ya sanya hannu domin fara aiwatar da wannan tsari.

Da yake yiwa jaridar PRNigeria ƙarin haske, Babban Ma’ajin Ƙungiyar NASSI na ƙasa, Dakta Abubakar Tanko Bala ya ce manufar shirin shine nema wa Mambobinta rancen da zasu inganta kasuwancin su.

Ya kuma ƙara da cewa an kasa tsarin gida Uku, ta yadda kashin farko za’a bawa masu manyan Masana’antu rancen naira Bilyan 75, sai ɓangaren su na masu ƙananan da matsakaitan Masana’antu inda suma zasu amfana da naira Bilyan 75, da kuma masu sana’oi na gida (Nano Program) su kuma zasu amfana da Naira Bilyan 50.

Bugu da ƙari ƙungiyar ta bayyana matuƙar farin cikin ta, a bisa yadda Bankin ya basu tabbacin cewa sune zasu fitar da Jadawalin waɗanda zasu amfana da wannan tsari na Rancen naira Bilyan 75 ga ƙananan da matsakaitan Masana’antun dake faɗin ƙasar.

Haka kuma yarjejeniyar ta ƙunshi yadda za’a wayar da kan masu ƙananan Masana’antu dama basu bitar yadda zasu inganta kasuwancin su ko kuma Kamfanoni dake faɗin ƙasar.

A cewar Dakta Tanko, “Wannan shiri na cikin Kyawawan ƙudirrikan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, na nemawa talakawan ƙasar mafita a sakamakon irin halin da aka tsinci kai a ciki na matsi da taɓarɓarewar tattalin arziƙi”.

domin haka ne ƙungiyar ta buƙaci dukkan Mambobin ta dake Jihohin Najeriya 36 da babban birnin tarayya Abuja su yi gaggawar shiga wannan tsari domin ya zamana sun ci gajiyar shirin ta yadda zasu bunƙasa harkokin kasuwancin nasu dama tattallin arziƙin ƙasar.

A ƙarshe Babban Ma’ajin ƙungiyar yayi fatan dukkan waɗanda suka sami wannan rance zasu yi amfani dashi ta hanyar da ta dace, kuma su dawo dashi cikin wannan lokaci da aka ƙayyade.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp