Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya yi Alla-wadai da harin da ƴanbindiga suka kai kan al’ummomin Munga Lelau a karamar hukumar Karim Lamido na jihar, abin da ya janyo mutuwar mutane da ba a san adadinsu ba.
Ƴanbindigar sun kai harin ne a lokacin da mutane ke komawa gida daga gonakinsu.
Lamarin ya afku da yammacin ranar Juma’a, makonni kalilan bayan wasu da ake zargin ƴanbindiga sun kashe wasu manoma biyu a yankin Bandawa na jihar.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Gwamna Kefas ya ce ba za a lamunci kai irin waɗannan hare-hare ba, inda ya ce suna mayar da jihar baya maimakon ci gaba.
Ya gargaɗi masu kai harin da cewa za su ɗanɗani kuɗarsu.
Ya kuma ƙara nanata cewa yana duk mai yiwuwa domin tsare jihar daga hare-hare da ake kai wa.
Ya ƙara da cewa akwai buƙakatar haɗa-kai tsakanin al’umma da jami’an tsaro, musamman wajen bayar da bayanan da suka kamata.











