Home Taska Matatar Dangote ta Dakatar da Amfani da Naira Wajen Sayar da Man...

Matatar Dangote ta Dakatar da Amfani da Naira Wajen Sayar da Man Fetur

Matatar Dangote

Matatar Dangote ta Dakatar da Amfani da Naira Wajen Sayar da Man Fetur

 

Masana sun yi gargaɗin cewa matakin na iya ƙara haifar da hauhawar farashin man fetur tare da rage darajar Naira.

Matatar Dangote ta sanar da cewa ta dakatar da amfani da Naira ta koma karɓar dalar Amurka wajen sayar da man fetur, dizal da kuma man jiragen sama.

Sabon tsarin wanda ya fara aiki nan take, zai shafi sayar da dukkan dangogin man fetur da ake ɗauka kai tsaye daga matatar da kuma waɗanda ake jigilar su ta ruwa.

Majiyoyi a masana’antar mai sun ce matakin ya biyo bayan yadda matatar ke sayen yawancin ɗanyen mai da dala, yayin da take sayar da man da ta tace a naira, lamarin da ya jefa ta cikin matsi na musayar kuɗi.

Wata majiya ta ce matatar na buƙatar fiye da jiragen ruwa 15 na ɗanyen mai a kowane wata, amma Kamfanin Man Fetur na Kasa NNPCL na iya samar da ƙasa da jirage uku kacal ne a ƙarƙashin yarjejeniyar sayen ɗanyen mai da naira.

Matakin kamfanin na Dangote da ke fitar da gangar mai 650,000 a kowacce rana ka iya haifar da hauhawan farashin man fetur tare kuma da rage darajar Naira wanda ka iya shafar masu karamin karfi.

Masana sun yi gargaɗin cewa matakin na iya ƙara haifar da hauhawar farashin man fetur tare da rage darajar Naira wanda hakan babu makawa zai shafi masu ƙaramin ƙarfi.

Masanin harkokin mai da iskar gas, Otunba Tunji Oyebanji, ya ce sauyin na nuna cewa yarjejeniyar sayen ɗanyen mai da naira ba ta gudana yadda aka tsara, saboda ƙarancin ɗanyen mai da ake samu da kuma yarjejeniyoyin da aka riga aka ƙulla na fitar da shi zuwa ƙasashen waje.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Haba, Abba Bichi — Waɗannan Tallace-Tallacen Ranar Haihuwa Sun Wuce Iyaka! Daga Yushau A. ShuaibNAF ta Kaddamar da Aikin Ceto Bayan Jirgin Saman Soja ya Fado a OndoSojoji Sun Kashe Mayakin B'Haram, Sun Kama Wani a GeidamRijistar Masu Kaɗa Kuri'a a Najeriya ta Kai Miliyan 103 - INECMuna Kafa Sabbin Sansanonin Sojoji Domin Kare Al'ummomin da ke Cikin Hatsari – TinubuJirgin Sojojin Sama (NAF) ya Fado a Ondo Dauke da Mutane 32Sojojin Najeriya Sun Kaddamar da Sabbin Bataliyoyi 3 Don Karfafa Tsaro a ZamfaraCOAS ya Nemi Karin Hadin Kan Sojoji da ECOWAS Kan Barazanar Ketare IyakokiSojoji Sun Kai Hari Sansanin Ƴan Ta'adda, Sun Kashe Mutum Ɗaya, Sun Kama Wanda Ake Zargi a Benue Yunwa da Tsananin Rayuwa Sun Sa Ƴan Tawaye 73 da Iyalansu Sun Mika Wuya — HQ TsaroDakarun Soji  Sun Ceto Sojan da Aka Sace a FilatoAn Tattara Bayanai Kan Hare-Haren Ta'addaci 367, An kashe Ƴan Ta'adda 52 a Watan SatumbaNajeriya @66: Gwamnatin Tarayya ta Karkata Kan Cigaba, Ayyukan Yi, da Inganta RayuwaNajeriya @66: Ministan Tsaro ya yi kira ga  Ƴan Najeriya da su Hada kai Domin Zaman Lafiya da TsaroPDP ta Zargi Gwamnatin Inuwa Yahaya da Shirya Katin Mambobi na Bogi Gabanin Zaben Fidda Gwani a Gombe
X whatsapp