Home Labarai Babban Hafsan Sojin Nijeriya , Ya Taya Sojojin Kasar Murnar Bikin Sallah.

Babban Hafsan Sojin Nijeriya , Ya Taya Sojojin Kasar Murnar Bikin Sallah.

Babban Hafsan Sojin kasa (COAS) Laftanar Janar Faruk Yahaya, ya taya Sojojin Nijeriya murnar bikin Sallah Kara.

Wannan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa mai dauke sa hannun daraktan yada labaran Rundunar Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, takardar dake da kwanan watan 29 ga watan Afrilun 2022, ta mabaci laftanar Janar Yahaya na kalaman yayin da yake mika sakon fatan alheri ga ma’aikatan rundunar sojin kasar nan a duk inda suke a fadin Nijeriyar da kuma yabawa bisa ga sadaukarwasu da jajircewar da suke nunawa akan ayyukan su na kare martabar Nijeriya.

Babban hafsan sojin a bukaci dakarun rundundar da su kara kaimi wajen cigaba da gudanar ayyukan alkhairin da suka gudanar a watan ramadan, tare kuda mayar da hankali wajen sauke nauyi da ya rataya a wuyan su kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya tanada.

Ya bukaci kwamandojin yakin da su rubunya kokarin si a cigaba da gudanar da ayyukan su, daga bisani ya bayyana cewa goron sallar da yake bukata dagagare su shine su tabbatar da sun kawar da ‘yan ta’adda masu garkuwa da mutane tare da kwato makamai daga hannun su.

Janar Yahaya ya yi amfani da damar wajen yin addu’a ga sojojin da suka rasa rayukan su wajen kare martaba da muhibbar Nijeriya.

Ya kuma kara cewar a karkashin shugabancin sa  jami’an zasu cigaba da samun horo tare da lura da iyalan su, inda ya bada tabbacin cigaban da baiwa wadanda sula sami rauni a yayin gudanar da aikin kare wannan kasa, tare da basu kulawa ta musamman da zata taimawa musu wajen dawo da lafiyar su kamar yadda suke a da.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp