Home Labarai Maulid: Ministan Tsaron Nijeriya Ya bukaci Addu’oi Domin Magance Rashin Tsaro

Maulid: Ministan Tsaron Nijeriya Ya bukaci Addu’oi Domin Magance Rashin Tsaro

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta bukaci Al’ummar musulmi dasu yi amfani da lokacin bukukuwan maulidu wajen yiwa kasar Addu’ar kan matsalolin tsaron da suka addabi Al’ummar ta.

Wannna na kunshe ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mataimaki na musamman ga Ministan tsaron Nijeriya Manjo Janar Bashir Salihi Magashi mai ritaya, kan harkokin sadarwa Mohammad Abdulkadri ya fitar domin taya Al’ummar Musulmi murnar Mauludin Fiyayyen Halitta na bana.

Yace haihuwar fiyayyen halitta ta zo wa da duniya da abubuwan da suka jibanci yadda za’ayi koyi da hakuri, addu’oi da Kankan da kai, gami da tsoron Allah, wadanda a cewar sa sun cancanci koyi ga dukkan musulmi da wadanda ba musulmi ba.

Ministan tsaron ya bukaci Al’ummar musulmi dasu yi amfani da wanna biki wajen rokowa kasar kyakkyawar makoma, ta hanyan yi mata add’oin samun zaman lafiya mai dorewa, gami da kasancewa cikin masu bada gudunmawar da ta dace wajen magance kalubalen tsaron da kasar ke fama da shi, tare da shiga cikin masu samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, wanda shine tushen addinin Musulunci.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp