Rikicin Hausawa da Wasu Kabilu yayi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 150 a Sudan

Rahotanni na bayyana cewa Akalla mutane 150 ne aka tabbatar da cewa sun rasa rayukansu ciki har da tarin kananan yara bayan share tsawon kwanaki biyu ana bata-kashi tsakanin Hausawa da kabilun da ke rayuwa a yankin kudancin jihar Blue Nile na kasar Sudan.

Rikicin wanda ya samo asali daga batun mallakar filayen noma da kiwo, shi ne mafi muni da aka fuskanta a baya-bayan nan tsakanin kabilun da ke zama a yankin na kudancin jihar Blue Nile.

An dai gwabza fadan na kwanaki 2 mai muni tsakanin kabilun a yankin Wad al-Mahi mai tazarar kilomita 500 da birnin Khartoum fadar gwamnatin kasar inda shugaban yankin Abbas Moussa ya tabbatar da cewa a ranakun Laraba da Alhamis mabanbantan kabilun sun farwa juna lamarin da ya kai ga jikkatar mutane akalla 86 baya ga dimbin rayukan fiye 150 da da suka salwanta galibi Mata da yara da kuma tsofaffi.

Tuni dai al’ummar yankin suka fara wata zanga-zangar bukatar kawo karshen rikicin tare da kira ga gwamnatin kasar kan ta sauke gwamnan jihar wanda suke zargi da assasa rikicin.

Masu zanga-zangar rike da allunan bukatar sauke gwamnan sun rika rera waken cewa basa bukatar tashin hankali da rikici.

Shirin Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ya yi gargadin yiwuwar fuskantar tashe-tashen hankula a yankin na Blue Nile sakamakon yadda makamai ke bazuwa a yankin wadanda ake shigar da su daga Habasha da kuma Sudan ta kudu dukkaninsu masu fama da yake-yake.

Babban jami’in Majalisar a Sudan Eddie Rowe ya ce tun farowar rikicin a ranar 13 ga watan nan akalla mutane 170 suka mutu yayinda wasu 327 suka samu munanan raunuka tsakanin kabilun biyu.

 

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 15 hours 11 minutes 23 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 16 hours 52 minutes 48 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com