Rahotannin daga kasar Iran na bayyana cewa Jami’an tsaro sun bude wuta kan dandazon masu zanga-zangar cika kwanaki 40 da kisan matashiya Mahsa Amini inda mutane da dama suka jikkata, ciki har da wadanda suka yi dafifi a kabarin matashiyar.
Dubunnan masu zanga-zangar kisan Mahsa Amini sun yi dafifi a kabarin matashiyar da ke yankin Saqez don jimamin cika kwanaki 40 da kisan da aka yi mata, duk kuwa da matakan tsaron da gwamnatin kasar ta sanya don hana gangamin a yau laraba.
Baya ga wadanda suka yi dafifi a makabarta da aka birne Mahsa wasu dubunnan masu zanga-zangar na daban sun taru a dandalin Zindan da ke cikin garin na Saqez a yammacin yankin Kurdawa lamarin da ya sanya jami’an tsaro bude wuta tare da amfani da hayaki mai sanya hawaye don tarwatsa dandazon.
Read Also:
Wani faifan bidiyo da tuni ya fara yawo a kafafen sada zumunta sun nuna yadda jami’an ‘yan sandan ke amfani da karfin wajen tarwatsa masu zanga-zangar, wanda wata kungiyar kare hakkin dan adam ta kasar Norway da ke sanya idanu a zanga-zangar ta Iran ke cewa matakin da jami’an suka dauka ya take dokokin hakkin masu gangamin.
Dubun-dubatar ‘yan kasar ta Iran galibi mata ne ke ci gaba da zanga-zanga don nuna bacin ransu game da kisan matsahiya Amini mai shekaru 22 kwanaki 3 bayan jami’an tabbatar da da a sun kame ta bisa laifin kin saka hijabi.
Fiye da wata guda ana ci gaba da zanga-zangar a sassan Iran wadda ta samu goyon baya daga kasashe daban-daban yayinda ta janyowa kasar karin takunkumai daga ketare, sai dai gangamin ya sake karfafa a yau ne dai dai lokacin da ake kammala makokin kwanaki 40 da bisa al’ada ake yiwa kowanne mamaci a Iran.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 18 hours 9 minutes 21 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 19 hours 50 minutes 46 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com