An bukaci kasashe masu karfin mawadata da su biya diyar kudade ga takwarorin su matalauta, sakamakon yadda suka haddasa aukuwar musibu masu nasaba da sauyin yanayi a kasashen nasu.
Wanan na zuwa ne bayan bude taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya mai take COP27 dake gudana a kasar Masar.
Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya mai tada hankali ya ce, shekaru takwas da suka shude na baya-bayan nan, sun zama mafi samun dumamar yanayi a tarihi, inda aka samu tumbatsar tekuna, narkewar tsaunukan kankara , tsananin zafi da dai sauran ibtila’o’in da ke nuni da sauyin yanayi.
Read Also:
Sakatere Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guteress ya ce, a daidai lokacin da aka bude taron na COP27, wannan doran duniyar da muke rayuwa a kai, na aikewa da mummunan sako.
A ‘yan watanni da ssuka gabata, ambaliyar ruwa ta yi barna sosai a kasashe irinsu Pakistan da Najeriya, sannan matsalar fari ta yi kamari a nahiyar Afrika da Amurka, yayin da kuma guguwa ta yi shara a yankin Caribbean, inda kuma aka samu wani irin zafi mai tsanani da ba a taba gani ba a nahiyoyi uku na duniya.
Taron na COP27 da ke gudana a wurin shakatawa na Sharm el-Sheikh da ke kasar Masar, na zuwa ne a daidai lokacin da ake gwabza yaki tsakanin Rasha da Ukraine, al’amarin da ya haddasa hau-hawan farashin kayyaki a sassan duniya.
Taron na bana zai fi mayar da hankali ne kan yadda za a tara kudaden tunkarar matsalar ta sauyin yanayi.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 18 hours 9 minutes 21 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 19 hours 50 minutes 46 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com