Home Labarai Shugabannin Kungiyar ASUU na Ganawar Gaggawa

Shugabannin Kungiyar ASUU na Ganawar Gaggawa

Shugabannin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya ASUU sun shiga ganawar sirri ta gaggawa.

An ruwaito cewa kungiyar ta shiga ganawar sirrin ne da tsakar ranar Litinin, a harabar sakatariyar kungiyar da ke jami’ar Abuja.

Ganawar karkashin jagorancin shugaban kungiyar Farfesa Emmanuel Osodeke, za ta duba batun biyan malaman rabin albashin watan Oktoba.

Tun da fari dai kungiyar reshen jami’ar Jos Sun dakatar da mambobin su da zuwa aiki har sai gwamnatin tarayya ta biya su cikakken Albashin su, duk da sun bayyana cewa ba yajin aiki suka shiga ba.

Sai dai daga bisani gwamantin Nijeriya ta Magantu kan  biyan su ALbashin na kwanaki 17 da suka yi aiki a cikin su, duk da abinda kungiyar ta kira alkawarin gwamantin tarayya ta dauka musu na biyan su Albashin watan na Oktoba cikakken.

Idan dai za’a iya tunawa kugiyar malaman Jami’oin Nijeriya ta tsunduma yajin aiki ne bisa abinda ta kira gazawar gwamnatin kasar na gaza biya mata bukatun da ta nema, yajin aikin da suka kwashe watanni 8 ba tare da sun shiga ajujuwan sub a domin koyar da dalibai.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp