Home DUNIYA AU na shirin kakabawa Chadi Takunkumi

AU na shirin kakabawa Chadi Takunkumi

Kwamitin zaman lafiya da tsaro na Tarayyar Afirka (PSC) ya fara wani muhimmin taro kan kasar Chadi domin nazari kan wani rahoton shugaban kungiyar kan rikice-rikicen baya-bayan nan da suka wakana baya ga duba yiwuwar kakabawa kasar takunkumi.

Mambobi 15 na wannan kwamiti da ke da alhakin kariya da warware rikice-rikicen kasashen Afirka za su yi nazari kan rahoton da shugaban gudanarwarta dan asalin kasar Chadi Moussa Faki Mahamat ya gabatar, rahotan da tuni ya yadu a kafofin sada zumunta tun gabanin gabatar da shi.

Rahotan mai shafuka takwas ya tabbatar da sahihancin sa, bashi da wani sauki ga mahuntan rikon kwaryar sojin Chadi karkashin jagorancin janar Mahamat Idriss Deby Itno.

Rahotan ya zargi gwamnatin rikon kwaryar Chadi da kin mutunta wa’adin watanni 18 na mika mulki ga fararen hula kamar yadda aka yi alkawari tun farko, kana sunyi biris da mutunta haramcin da aka sanya wa sojojin da ke kan mulki shiga takara a zabe mai zuwa, abin da shugaban hukumar ta AU Moussa Faki ke ganin biri ne yayi kama da mutun, don haka babu wani zabi face kakaba musu takunkumi.

Tuni wata majiya mai tushe ta tabbatar da fushin Ndjamena tun bayan yaduwar rahoton, inda suka ce kungiyar ci gaban tattalin arzikin kasashen Tsakiyar Afirka ke bibiyar lamuran ba hurumin AU ba.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp