WHO: Ebola ta Kashe Mutu 54 a kasar Uganda

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce cutar Ebola ta kashe mutane da yawansu ya kai 54 cikin kwanaki 55 da bullarta a Uganda, dai dai lokacin da ake ci gaba da samun karuwar masu harbuwa da cutar.

Cikin rahoton da WHO ta fitar kan yadda cutar ta Ebola ke ci gaba da lakume rayuka a Uganda, ta ce yankin Mubende da ke tattara alkaluman na da mutane 29 cikin mutanen 54 da cutar ta kashe.

A cewar rahoton daga lokacin da cutar ta bulla a ranar 20 ga watan Satumba zuwa yanzu an samu mutane 137 da aka tabbatar sun kamu da ita yayinda wasu 65 kuma suka warke.

Hukumar ta WHO ta ce yankunan da cutar ta fi yaduwa a sassan Uganda sun kunshi Kassanda da Kyegegwa da kuma Kagadi baya ga Bunyangabu da Wakiso da kuma Masaka da Kampala.

WHO ta ce yankunan Mubende da Kassanda inda ta fi tsananta na jumullar mutum 63 da kuma 47 da zuwa yanzu ke jinyar cutar ta Ebola.

Dukkanin yankunan dai yanzu haka na karkashin killacewar kwanaki 21 a kokarin dakile yaduwar cutar, wanda ya sa tun daga ranar 10 ga watan nan ba a sake samun wanda ya harbu ba.

Cikin mutane dubu 2 da 187 da aka yi imanin sun yi mu’amala da masu dauke da cutar, sun kammala killacewar kwanaki 21 karkashin kulawar jami’an lafiya kuma mutum 1 da 908 basu harbu da cutar ba.

 

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 13 hours 33 minutes 29 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 15 hours 14 minutes 54 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com