Home Labarai Bincike: Kashi 65% Na Talakawan Nijeriya na Zaune ne a Arewancin Kasar

Bincike: Kashi 65% Na Talakawan Nijeriya na Zaune ne a Arewancin Kasar

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta bayyana cewa kashi 63 cikin 100 na mutanen Najeriya kusan miliyan 133 na fama da komajin talauci.

An gabatar da wannan adadi ne yayin kaddamar da bincike kan Talauci na Najeriya na Multidimensional Poverty Index (MPI) a birnin Abuja ranar Alhamis.

PRNigeria ta ruwaito cewa, ma’aunin da aka yi amfani da shi wajen kididdige wannan adadi ya samo asali ne a kan Multidimensional Poverty Index (MPI) Inda Akai la’akari da bangarori biyar cikin wadanda suka hadar da kiwon lafiya, yadda ake rayuwa, da ilimi, gami da tsaro da kuma rashin aikin yi.

Binciken wanda aka yi samfuri da gidaje sama da 56,000 a fadin Jihohi 36 na kasar gami da Babban Birnin Tarayya Abuja, wanda aka gudanar tsakanin watan Nuwamba 2021 zuwa Fabrairu 2022, ya nuna cewa kashi 65 cikin 100 na talakawan kasar, miliyan 86, suna zaune ne a Arewa, yayin da kashi 35, kusan Miliyan 47 suna zaune a Kudu.

Binciken ya bayyana jihar Sokoto a matsayin jihar da  tafi kowacce jiha yawan masu fama da talauci a fadin ƙasar,  inda take da kashi 91 cikin dari yayin da Ondo ke da kaso 27 cikin dari.

Da yake jawabi a wajen taron, shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya ce an dauki matakin ne don gano adadin masu fama da talauci da kuma hanyoyin da Za’a fito da manufofi Masu kyau don kawar da talaucin a cikin al’umma.

Buhari wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan fadar sa Farfesa Ibrahim Gambari.

Rahoton ya kara da cewa, “sama da rabin al’ummar Najeriya talakawa ne da suke amfani da kawayi ko ita ce wajen yin girki maimakon makamashi mai tsafta.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp