Wani Farmakin Hadin Gwiwa tsakano Congo da Burundi ya halaka mayaka 40

Rahotannin na bayyana An halaka ‘yan tawayen Burundi 40 a wani farmakin hadin gwiwa da sojojin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da Burundi suka kai a gabashin Congo.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Laftanar Marc Elongo-Kyondwa ya ce sojojin biyu “sun kai wani gagarumin farmaki” kan ‘yan tawayen Burundi.

Ya kara da cewa sojojin biyu sun fatattaki ‘yan tawayen FNL daga dukkan tsaunuka hudu da ke yankin Nabombi.

Sanarwar ta ruwaito Janar Ramazani Fundi, kwamandan ayyuka a yankin kudancin kasar Congo yana cewa, rundunar sojojin Congon ta yi kira ga al’ummar yankin da su ba da hadin kai ga sojojin, sannan kuma matasa su ware kansu daga kungiyoyin da ke dauke da makamai”.

Tun a watan Agusta, sojojin Burundin ke yaki da kungiyoyin masu dauke da makamai a yankin Kivu ta Kudu, a matsayin wani bangare na rundunar kungiyar kasashen gabashin Afirka (EAC).

A cikin watan Yuni, EAC ta yanke shawarar kafa rundunar yankin da ta kunshi sojojin Kenya da Uganda tare da sojojin Congo a arewacin Kivu da Ituri, da sojojin Sudan ta Kudu da ke Haut-Uele da kuma Burundi a kudancin Kivu.

Kinshasa da ke zargin Rwanda da goyon bayan ‘yan tawayen M23 a arewacin Kivu, ta ki yarda Kigali ta shiga cikin rundunar.

Kimanin shekaru 30 kenan gabashin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo ke fama da kungiyoyin masu dauke da makamai, wasu na cikin gida, wasu kuma daga kasashe makwabta.

 

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 14 hours 22 minutes 19 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 3 minutes 44 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com