Home General Dakarun sojojin Nijeriya sun Murkushe ‘Yan Ta’adda a Mafa ta Jihar Borno

Dakarun sojojin Nijeriya sun Murkushe ‘Yan Ta’adda a Mafa ta Jihar Borno

Dakarun sojin Nijeriya karkashin rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) a Arewa Maso Gabas sun sami Nasarar tarwatsa gungun ‘Yan Boko Haram a wani kwanton Bauna da suka yi musu a kauyen
Troops of Operation kauyen Ngowom dake karamar Hukumar Mafa ta jihar Borno.
Gungun ‘yan ta’addan da aka hallaka Su 20 dake saman babura sun fito daga
Yammacin jihar ta mashiga Mafa akan hanyar su ta zuwa dajin Sambisa.
Zagazola ya ruwaito cewa dakarun sojin sun sami nasarar ne bayan samun wani rahoton sirri kan cewa ‘yan Ta’addan na kan hanyar Mafa
Sojojin bisa hadin Gwiwar dakarun sa kai na JTF suka yi musu kwanton bauna, nan take suka hallaka da dama cikin su.

Haka kuma sun sami nasarar kama guda cikin ‘yan Ta’addan a raye, yayin da wasu suka gudu cikin daji da raunin harbi a jikin su.
“kwanton baunar ya haifar da mummunar musayar wuta tsakanin mu, daga bisani sun fara shirin ranta a na kare, na muka bisu, saboda haka mun halaka da dama daga cikin su, wasu kuwa sun tsere da raunikan harbi a jikin su. A cewa majiyar.
Ya bayyana cewa 2 cikin dakarun CJTF sun ji rauni sakamakon musayar wuta, inda kuma suka sami nasarar kwato makamai da babura a hannun ‘yan Ta’addan

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp