Home General Wasu ‘yan bindiga a jihar Imo sun sare kan wani shugaban...

Wasu ‘yan bindiga a jihar Imo sun sare kan wani shugaban ƙaramar hukumar Ideato ta arewa a jihar

Wasu ‘yan bindiga a jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya sun sare kan wani shugaban ƙaramar hukumar Ideato ta arewa a jihar, bayan da suka sace shi a ranar Juma’ar da ta gabata.

‘Yan bindigar dai sun saki wasu hotunan bidiyo da ke nuna yadda suka ɗaure shugaban ƙaramar hukumar a hannaye, da kuma yadda suka halaka shi, bayan sun karɓi kuɗin fansa don su sako shi.

Wata majiya a rundunar ‘yan sandan Najeriya ta jihar Imo, ta tabbatar wa BBC labarin kisan gillar da ‘yan bindigar suka yi wa shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Ideato ta Arewa a jihar, mai suna Chris Ohizu, ƙasa da kwana biyu da sace shi.

Majiyar ‘yan sandan ta ce, rundunarsu tana ƙoƙarin ceto shugaban ƙaramar hukumar daga hannun ‘yan bindigan da suka sace shi, sai kwatsam a daren Lahadi aka yi aune da wasu hotunan bidiyo da ke nuna yadda aka durƙusar da shi kan gwiwoyinsa, a wani ƙungurmin daji, aka ɗaure masa hannaye a harɗe ta baya, daga bisani kuma aka sare masa kai.

Amma dai rundunar ‘yan sandan ta bayar da tabbacin tana ci gaba da gudanar da bincike, har sai ta zaƙulo waɗanda ake zargi da tafka wannan aika-aika.

A ɗaya daga cikin hotunan bidiyon da suka karaɗe shafukan sada zumunta, da ‘yan bindigan suka saki, an ji wata murya tana barazanar halaka shi kansa gwamnan jihar ta Imo, Hope Uzodimma nan ba da daɗewa ba.

Muryar ta kuma ce, su ba ‘yan kungiyar tsaro ta ESN ko kungiyar ‘yan a-waren Biafra ta IPOB ba ne. Su dai gungun wasu mutane ne da ke fafutukar tabbatar da kafuwar jamhuriyyar Biafra a yankin kudu maso gabashin Najeriya, inda suka lashi takobin ba za su bari a gudanar da babban zaben da ke tafe ba.

Ko da a ranar Juma’ar da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga suka sace shugaban ƙaramar hukumar na riƙo, bayan sun harbe shi da bindiga a kafa, sannan suka banka wa gidansa wuta.

Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto dai gwamnatin jihar Imo ba ta ce uffa ba, game da aukuwar wannan lamari.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp