Dakarun rundunar ta civil Defence shiyyar jihar Zamfara ta kama masu garkuwa da mutane su 4 da ake zargin sun yi garkuwa da yaro dan shekara 2 a ranar 21 ga watan Janairu 2023 a Angwa Shado dake kwaryar Gusau.
Wannan na kushe a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar Ikor Oche SC ya fitar a madadin Kwamandan shiyyar.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Sanarwa tace a yayin da ake holen mutanen kwamandan rundunar na jihar Zamfara Muhammad Bello Muazu yace an kama wadanda ake zargin da hannu wajen yin garkuwa da yarinya mai kimanin shekaru 2 mai suna Hawau Masaud tare da ‘yar Uwarta Umalkaidi Shahibilu mai shekaru 13 da haihuwa.
Ummulkhairi tayi bayanin cewa wani dake sanye da bakaken kaya ya kwace kwanwarta inda ya shiga cikin wani kango da ‘yan uwa sa ke buye, inda daga bisani aka bayya sunan sa da Muslim Sani.
PRNigeria hausa












