Home General Bankunan kasuwanci sun dakatar da ayyukansu a Akure babban birnin jihar Ondo

Bankunan kasuwanci sun dakatar da ayyukansu a Akure babban birnin jihar Ondo

Bankunan kasuwanci sun dakatar da ayyukansu gaba daya a Akure babban birnin jihar Ondo da ke kudu maso yammacin Najeriya.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa dukkanin bankunan da wakilanta suka ziyarta a titin Oba Adesida da kuma Alagbaka a babban birnin jihar, kofofinsu na kulle.
Sai dai ta ce akwai tarin jama’a masu mu’amulla da bankin da suke tsaye curko-curko a wajen bankunan suna zaman jiran tsammani.
Daya daga cikin mutanen mai suna Jimoh ya bayyana cewa tun karfe 7:30 nsf (na safe) yake wurin.
Mutumin ya ce jami’an tsaron bankunan sun gaya masa cewa an rufe bankunan ne saboda tsoron kai musu hari.
kamar dai sauran sassan jihar ta Ondo can ma a garin Ikare-Akoko da ke yankin karamar hukumar Akoko Northeast ba a bude bankunan ba ga jama’a.
Jama’a na fama da wahalhalu sakamakon matakin Babban Bankin kasar na sauya fasalin wasu daga cikin manyan takardun kudin kasar na 1,000 da 500 da kuma 200.
Bankin ya sanya wa’adin daina karbar takardun a tsakanin jama’a zuwa ranar 10 ga watan nan na Fabrairu, to amma kuma a jiya laraba Kotun Kolin kasar ta yanke hukuncin shari’ar da gwamnonin jihohin Kogi da Kaduna da kuma Zamfara suka shigar gabanta kan hana wa’adin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp