Home General Dakarun Sojojin Nijeriya sun tarwatsa maboyar ‘yan bindiga a jihar Kaduna

Dakarun Sojojin Nijeriya sun tarwatsa maboyar ‘yan bindiga a jihar Kaduna

Dakarun sojojin Najeriya rukuni na huɗu da wasu dakaru na musamman na bataliya ta 167 sun kashe ‘yan bindiga tare da ceto mutane 14 da aka yi garkuwa da su a Jihar Kaduna.

Dakarun waɗanda suka shafe dogon lokaci suna bata kashi da ‘yan bindigar a yankin Ƙaramar Hukumar Chikun sun tashi wata maɓoyar ‘yan bindigar a lokacin rikicin.

Wannan na Cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida Samuel Aruwan ya fitar, inda yace “yayin wannan samame an ceto mutane 14, da suka hadar  da maza tara da mata biyar. An kai waɗanda aka ceto ɗin wani wuri mai aminci za a yi musu gwaje-gwaje kafin a haɗa su da iyalansu.”

A cewarsa a yayin wannan simamen, dakarun sun lalata sansanin ‘yan bindiyar da dama an kuma kwato wasu motoci biyu.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp