Gwamnatin sojin kasar Mali ta sanar da dage Shirin yiwa kundin tsarin mulkin kasar gyaran fuska da aka tsara gudanarwa a ranar 19 ga watan Maris din da muke ciki, yayin da ta kara jaddada alkawarin da ta yin a mika Mulki hannun farar hula a shekarar 2024.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Gwamnatin ta sanar da wannan hukunci ne ta hanyar kafa nada wakilai daga hukumar zabe a dukkanin shiyyoyin kasar, da nufin yada sabon kundin tsarin mulkin kasar sassan kasar domin su kai hannun al’umma kai tsaye.
Samar da kundin tsarin Mulki a wannan lokaci dais hi ne zai baiwa sojojin dake Mulkin kasar dake fama da ayyukan masu ikirarin jihadi, damar cigaba da jan ragamar shugabancin kasar har zuwa shekarar 2024 kamar yadda suka alkawarta.
PRNigeria hausa











