Shugaban Hukumar Tarayyar Afirka, Moussa Faki Mahamat, ya fitar da wata sanarwa kan abin da ke ci gaba da faruwa a Sudan.
Sanarwar ta ambato shugaban Tarayyar Afirka na roƙon “ɓangarorin siyasa da soji su samo mafitar siyasa ta adalci ga rikicin da ya taso bayan juyin mulkin 25 ga watan Oktoban 2021 da kuma miyagun abubuwan da suka biyo baya.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Mahamat na magana ne kan abin da ke faruwa game da ranar da sojojin Sudan ƙarƙashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhan suka ƙwace iko da gwamnati a Sudan.
Sanarwar Mista Mahamat ta yi kira ga sojoji da kuma dakarun RSF masu kayan sarki cewa: “Cikin gaggawa a dakatar da ruguza ƙasar, da tafka ta’addanci ga al’ummarta, da kuma zubar da jini a wannan lokaci na goman ƙarshe cikin watan Ramadan mai alfarma”.
An dakatar da Sudan daga ƙungiyar ƙasashen ta Tarayyar Afirka a watan Yunin 2019.











