Home General Gwamnatin jihar Gombe ta ce ta inganta Asibitocin PHCs a jihar

Gwamnatin jihar Gombe ta ce ta inganta Asibitocin PHCs a jihar

Gwamnatin jihar Gombe ta ce ta inganta asibitocin kiwon lafiya daga matakin farko na (PHCs) a wani yunkuri na inganta harkokin lafiya  a jihar da kuma inganta manyan asibitoci domin inganta bangaren lafiya.

Kwamishinan lafiya na jihar, Dr Habu Dahiru, ne ya bayyana hakan yayi  da yake ganawa da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya wato NAN a wata ziyarar gani da ido da kamfanin ya kai ranar alhamis.

Haka kuma kwamishinan ya kara da cewa a wani shirin hadin gwiwa da gwamnatin jihar tayi da Asusun tallafawa kananan yara na majalisar dinkin duniya, (UNICEF) wanda aka gyara asibitocin kiwon lafiya daga matakin farko (PHC) guda 114 domin kara karfafawa gami da inganta matakin lafiyar.

A cewar Mr. Dahiru, gwamnatin jihar na gudanar da aikin jinya don gano tare da tura ta tura yara masu fama da lalurar tamowa da mata masu juna biyu da ba basa samun damar zuwa asibiti domin haihuwa ta hanyar daukar matakai da dama.

Yace sama da ma’aikatan lafiya 600 da suka hadar da Ungozoma, ma’aikatan lafiyar al’umma, CHEW, aka tura zuwa asibitocin na matakin farko PHC a fadin kananan hukumomin jihar 11.

Daga bisani ya tabbatar da cewa daukar wannan mataki ya taimaka wajen rage yawan mutuwar nata masu juna biyu a fadin jihar.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp