Kotun ƙolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Lawal Dare na jam’iyyar PDP a matsayin gwamnan jihar Zamfara.
Kotun ƙolin ta yi watsi da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da ta ayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammalu ba inda ta ba da umarnin a sake gudanar da zaɓe a ƙananan hukumomi uku.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Hukumar zaɓe dai ta ayyana Dauda Lawal a matsayin wanda ya yi nasara da ƙuri’a 377, 726, inda a wani lamari mai cike da ban mamaki, ya kayar da gwamna mai ci Bello Matawalle.
Sai dai ɗan takarar na APC, Bello Matawalle wanda yanzu shi ne ƙaramin ministan tsaron Najeriya, ya zargi Inec da kassara nasarar da ya samu, saboda ta gaza haɗawa da sakamakon wasu mazaɓu.
PRNigeria hausa












