Home General Fashewar wani abu tayi sanadiyyar mutuwar yara 6 a jihar Borno

Fashewar wani abu tayi sanadiyyar mutuwar yara 6 a jihar Borno

fashearwa wani abu yayi sandiyyar mutuwar wasu yara a shida a karamar hukumar Gubio, da ke jihar Borno a rewa maso gabashin Nijeriya.

rundunar ‘yan sandna jihar ta bakin kakakinta ASP Nahun Daso ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta ce fashewar ta faru ne a wani gini da ke makarantar Islamiyya a ranar Asabar.

rundunar ta ce an tara wasu kayayyakin gwan-gwan da aka yi rashin sa’a wasu matasa da suka je wajen suka taru, a nan ne kuma aka samu abubuwan fashewa da suka tashi.

Rahotanni sun ce yaran kan tara ƙarafa da kuma sayar wa al’ummar yankin.

Duk da haramcin da aka yi kan sana’ar gwan-gwan, har yanzu ana cinikin lalatattun karafa a yankin da ke fama da tashe-tashen hankula na masu tayar da ƙayar baya.

ASP Nahun ya ce suna wayar da kan mutane game da “na’urorin fashewa” tare da hana saye da sayar da kayan gwan-gwan. Ya kuma kara da cewa rundunarsu za ta yi bincike a kan lamarin.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp