Gwamman ma’aikatan jinya da ungozama ne suka hau titunan birnin Abuja domin nuna kin amincewarsu ga wasu sabbin dokoki da hukumar kula da ma’aikatan jinya da ungozoma ta kasa ta shimfida musu.
Sabbin dokokin dai sun hadar da kwashe shekaru biyu wadanda suka karanci aikin jinya a jami’a suna aiki a Najeriya kafin hukumar ta tantance su a matsayin kwararrun ma’aikatan jinya. Hukumar ta kuma kara kudin tantancewar daga dubu 29 zuwa dubu 300.
To sai dai kungiyar ma’aikatan jinyar ta ce kudin ya yi yawa kasancewar a cikinsu akwai wadanda suke daukar albashin da bai wuce naira dubu 50 ba a wata.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Ma’aikatan lafiya dai a Najeriya na yawan ficewa daga kasar da zarar sun samu lasisin aiki zuwa wasu kasashen ketare.
Sau da dama dai ma’aikatan lafiya a Najeriya na kokawa kan rashin isasshiyar kulawa da suke samu ciki har da albashi.
PRNigeria Hausa












