Home Labarai ‘Yan bindiga sun yi awon gaba da dalibai sama da 100 a...

‘Yan bindiga sun yi awon gaba da dalibai sama da 100 a jihar Kaduna

An sace ɗaliban firamare da na sakandare kusan su 200 a makarantarsu da ke ƙauyen Kuriga a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna a arewa maso yammacin Najeriya.

Lamarin ya faru ne da safiyar yau (Alhamis) lokacin da ɗaliban ke taro (assembly) da misalin karfe takwas da rabi.

Wani babban jami’in gwamnatin jihar Kaduna ya tabbatar wa manema labarai afkuwar lamarin amma ya ce ya zuwa yanzu babu cikakken bayani kan lamarin.

Wani da ya shaida faruwar lamarin ya ce “yau da misalain ƙarfe 8:30 an gama asambili ke nan sai ga shigowar waɗannan mutane (ƴan fashi) daga kowane ɓangare, suka zo suka yi wa makarantar ƙawanya suka kwashi ɗalibai na firamare da sakandare kusan 200 suka wuce da su, har da malami ɗaya na sakandare”.

Shaidan ya kuma ce maharan sun harbi yaro ɗaya wanda aka garzaya da shi asibitin da ke garin Birnin Gwari.

Yaran da lamarin ya rusta da su, kamar yadda shaidan ya tabbatar shekarunsu sun kama ne daga takwas zuwa 15.

Ko a watan Janairun shekarar nan, wasu ƴan bindiga sun shiga ƙauyen na Kuriga, inda suka kashe shugaban makaranta tare da sace matarsa.

Kuriga ƙauye ne da ke kan babbar hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari, yankin da ya yi ƙaurin suna wajen ayyukan ƴan fashin daji.

A shekarar 2023 ƴan bindiga sun kai hari kan sojojin da ke sintiri a kan hanyar tare da ƙona mota mai sulke.

Sace-sacen ɗalibai irin wannan na tuno wa al’ummar Najeriya da satar ƴanmatan makarantar sakandaren Chibok da ke jihar Borno, inda a daren 15 ga watan Afrilun 2014 mayaƙan Boko Haram suka kai farmaki a makarantar tare da sace ɗalibai sama da 200.

PRNIgeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp