Atiku ya gargadi Tinubu kan tauye hakkin ‘yan Jaridu a Nijeriya

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa karkashin inuwar jam’iyyar PDP a zaben shekara ta 2023 da ta gabata, Alhaji Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da yunkurin gwamnatin jam’iyyar APC mai mulkin  karkashin jagorancin Bola Tinubu, na murkushe yancin yada labarai da kafafen yada labarai ke da shi kundin tsarin mulki kasa na 1999 da aka yiwa gyaran fuska.

wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da Alhaji Atiku Abubakar ya fitar kuma aka raba ga manema labarai. inda tace da ayyana yunkurin gwamnatin matsayin wata barazana ga harkokin yada labarai.

 

“Ba karamar barazana ba ce ga tabbatar da dimokaradiyyar Nijeriya, wadda ta ke damfare akan durakun bangarori guda hudu na zartarwa, dokoki, Shari’a da na yan jarida wadanda hakkin sanar da al’umma halin da kasa ta ke ciki ya rataya a wutansu”.

 

Atiku Ya yi kira ga yan jarida a kasar da cewa kada su bari wannan barazanar ta tsorata su, ta yadda zasu kasa sanar da al’umma rawar da gwamnatin da ke mulkinsu ke takawa wajen tasarrafi da al’amuran da suka shafi rayuwar su da walwalar su.

Idan za’a iya tunawa gwamnatin tarayyar Nijeriya na shan suka tun bayan da jaridar Daily Trust ta wallafa labarin kan batun yarjejeniyar Samoa da gwamantin Nijeriya, wadda ake zargin cewa akwai batun auren jinsi a cikin ta.

Lamarin da yasa gwamnatin tarayyar ta musanta, har ma ya ti barazanar daukar matakin Shari’a kan Kamfanin jaridar Daily Trust.

PRNigeria hausa

 

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 9 hours 26 minutes 32 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 11 hours 7 minutes 57 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com