Home DUNIYA Ku daina bayyana kan ku matsayin sarakai – Umarnin Kotu ga ...

Ku daina bayyana kan ku matsayin sarakai – Umarnin Kotu ga Tsofaffin Sarakunan Kano

Majalisar jihar Kano
Majalisar jihar Kano

Babbar kotun jaha mai lamba 7 karƙashin jagorancin mai shari’a Amina Adamu, ta tabbatar da ingancin  dokar da majalisar jihar Kano ta samar wadda ta rushe sarakuna biyar da aka samar a cikin tsohowar doka.

Kotun ta ayyana cewar dokar masarautu ta shekarar 2024, wadda majalisar dokokin kano ta samar a matsayin dai-dai.

Da take yanke hukuncin a zaman ta na yau, kotun ta kuma bayyana cewar aikin majalisar dokoki shine ta yi doka, ko ta rushe doka, ko kuma ta yiwa doka gyaran fuska.

Mai shari’a Amina Adamu, ta kuma bayyana cewar Sarakunan Kano waɗanda gwamnati ta cire kada su kara kiran kansu a matsayin sarakuna, kuma su dawo da dukkanin wata kadara mallakin gwamnati wadda take hannunsu.

 

Har ila yau, kotun ta ayyana cewar jibge jami’an tsaro a gidan sarki na Nassarawa da akayi ya saɓawa doka.

 

Tun da fari gwamnatin jihar Kano ce ta shigar da ƙarar inda ta roki kotun da ta tabbatar da dokar majalisa ta 2024.

Majalisar dokokin Kano dai ta yi wa dokar masarautu gyaran fuska wanda hakan ya dawo da masarauta guda ɗaya a jahar Kano.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp