CISLAC ta bukaci Gwamnatin Nijeriya ta magance matsalar yunwa a kasar

Kungiyar Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam da Kuma Sanya Idanu akan ayyukan Yan Majalisun Ƙasar nan CISLAC, ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta fito da Tsare Tsare da Zasu Amfani al’ummar Kasa maimakon Kara ta’azzara Zanga Zanga.

Wannan na cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar Auwal Musa Rafsanjani ya Fitar, wadda tace Wajibi ne Gwamnati Ta Dauki Matakin Gaggawa a bangarorin, Yunwa – Rashin aikin yi- Matsalar Tsaro – hau- hawar Farashin kayayyaki – Cin hanci da rashawa Wanda Sune Suka zubar da kimar Hukumomin Gwamnati

Ya Kara da Cewa Daukar matakin gaggawa a Wadannan bangarorin shine Zai baiwa Yan Nigeria kwarin Gwiwar Jin Cewa shugabanin Ƙasar sun damu da halin da suke Ciki.

kwamarade Auwal Musa Rafsanjani yace Wajibi ne Gwamnatin Tarayya da jami’an tsaro su baiwa al’umma kariya Yayin Gudanar da Zanga Zangar Lumana Kamar Yadda Tsarin Mulki ya Tanadar

Kwamarade Rafsanjani ya Kuma Gargadi Jami’an Tsaro na soji da Cewa su Kaucewa Shiga duk Wani hurumin da ba nasu ba, Inda Yace Yan Sanda da Kuma Jami’an Tsaro na Farin Kaya DSS Sune da Alhakin Sanya Idanu akan Yadda Zanga Zangar Lumana Zata Kasance

akashe ya Bukaci Masu Zanga Zangar da su Tabbatar Cewa Wasu Batagari basuyi Amfani dasu Wajen Tayar da tarzoma ba, Dan haka Yace Wajibi Masu Zanga Zangar su Sanya Idanu Sosai

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 4 hours 28 minutes 16 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 6 hours 9 minutes 41 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com