Gwamnatin jihar Kano ta shigar da sabuwar kara dake tuhumar tsohon Gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje da Murtala Sule Garo da wasu mutane biyu.
Acewar takardar karar, ana tuhumar Murtala Garo da Lamin Sani da Muhammad Takai da hada kai wajen aikata laifi da zanba cikin aminci da gabatar da bayanan karya da badakalar kudade.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Gwamnatin na zarginsu da wawure kudin kananan hukumomi dake asusun hadaka tsakanin jihar da kananan hukumomi 44.
Sannan ana zargin badakalar kudi ta Naira Biliyan 57.4 da suka karkatar dasu zuwa asusun ajiya na kashin kai.
Haka kuma ana zargin sun sauya kudin zuwa Dalar Amurka.
Haka kuma, gwamnatin na tuhumar su da mallakar kadarori da kudaden a kasar Dubai da Otel a garin Abuja da wasu gidajen mai a Kano.
Gwamnatin dai ta ce zata gabatar da shaidu 143 a gaban kotun a lokacin shari’ar.
PRNigeria Hausa












