Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa bashi da masaniya kan kwangilar samar da magunguna a kananan hukumomi 44 na jihar.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
wannan na cikin wata Sanarwar da kwamishinan yada Labarai na jihar Baba Halilu Dan Tiye ya fitar wadda aka rabawa manema labarai, ta ce Gwamnan Abba ya umurci Shugaban Hukumar karbar Korafe-korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano da ta gaggauta bincikar wannan zargi tare da bayar da rahoton sakamakon da ya dace domin daukar matakin da ya dace.
Sanarwar ta ci gaba da cewa manufar binciken shine bankado gaskiyar Lamarin domin tabbar da gaskiya da rikon amana wajen gudanar da shugabanci na gari ga alummar Kano baki daya.
Daga bisani Gwamna Yusuf ya kuma bukaci daukacin al’ummar Kano da su yi hakuri har a kammala bincike.
PRNigeria Hausa












