NNPCL ya bawa ‘Yan Nijeriya hakuri kan karancin Man fetur

Kamfanin mai na Nigeria NNPC ya ce ya damu matuka bisa yadda ake fuskantar karancin man fetur a wasu sassan Nigeria.

Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da babban jami’in sadarwa na kamfanin Olufemi Sonete ya fitar wadda aka raba manema labarai.

Ta cikin sanarwar NNPCL ya danganta matsalar da kalubalen aiki rarraba man fetur din a fadin kasar.

Haka kuma sanarwar tace NNPCL yana kira ga masu ababen hawa da su kara hakuri, yana aiki ba dare ba rana tare da masu ruwa da tsaki don shawo kan matsalar.

Al’ummar wasu sassan Nijeriya dai na fuskantar ƙarancin man fetur wanda hakan ya sanya ake sayar da man daga kan Naira 800 har yanzu Naira 950.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 18 hours 41 minutes 12 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 20 hours 22 minutes 37 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com