Ƙaramin ministan tsaro na Najeriya, Bello Matawalle ya sha alwashin cewa za a zaƙulo tare da hukunta duk masu hannu a kisan Sarkin Gobir na Gatawa da ke jihar Sokoto, Isa Bawa.
A ranar Laraba ne labarin kisan sarkin ya fito bayan ya kwashe sama da mako uku a hannun ƴan bindiga.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun daraktar ƴaɗa labaru ta ofishin ministan, Henshaw Ogubike, Matawalle ya yi tir da kisan sarkin, tare da bayyana hakan a matsayin “aikin rashin imani kuma abin da ba za a amince da shi ba.”
Ya ƙara da cewa “za mu yi iyakar bakin ƙoƙarinmu domin ganin an hukunta waɗanda ke da laifi a lamarin”.
Takardar ta ce Matawalle ya umarci shugaban hafsoshin tsaron Najeriya ya ƙaddamar da bincike kan kisan nan take tare da tabbatar da ganin an hukunta duk wadanda ke da hannu cikin lamarin.
Ta ƙara da cewa “za mu yi bincike na ƙwaƙwaf wajen ganin an hukunta waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki.”
A jiya Alhamis ne dai aka gudanar da sallar janaza ta ‘Salatul Ga’ib’, ga sarkin na Gobir, wanda ƴan bindiga suka hallaka, kasancewar ba a samu gawarsa ba.
Sai dai an samu nasarar karɓo ɗan marigayin, wanda ƴan bindiga suka ce su tare, wanda yanzu haka yake karɓar kulawa a asibiti.
Matsalar masu satar mutane domin neman kudin fansa na ci gaba da addabar jihohin arewa maso yammacin Nijeriya, duk kuwa da ƙoƙarin da hukumomi suka ce suna yi wajen tabbatar da tsaro.
Sai dai kisan sarkin na Gobir na daga cikin munanan abubuwan da suka faru a kwana-kwanan nan da ke nuna cewa har yanzu ƴan bindigar na ci gaba da cin karensu babu babbaka.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1255 days 15 hours 42 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1237 days 16 hours 42 minutes 7 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com