Najeriya ta yi asarar abincin da zai ciyar da mutum miliyan takwas a 2024 – FAO

Hukumar abinci da bunƙasa aikin noma ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce Najeriya ta tafka asarar tan 55,629 na abinci saboda ambaliyar ruwa a 2024.

Ƙididdigar da hukumar ta fitar ta nuna cewa asarar kayan abinci da aka tafka a Najeriya a bana ta isa a ciyar da mutum miyan takwas da rabi har tsawo wata shida.

Mataimakin shugaban hukumar a Najeriya, Salisu Mohammed, ya ce ɗumamar yanayi da hauhawar farashi da matsalar tsaro da kuma taɓarɓarewar tattalin arziki, na daga cikin abubuwan da suka addabi ɓangaren noma a Najeriya cikin shekarar nan.

Wannan ƙididdiga na zuwa ne albarkacin bikin Ranar Abinci ta Duniya, wanda ya mayar da hankali ga kira ga gwamnati ta haɗa hannu da ƙwararru wajen magance ƙalubalen ƙarancin abinci mai gina jiki a tsakanin al’umma.

Hukumar ta bayyana gamsuwa da matakan da gwamnati ke ɗauka wajen wadata ƙasa da abinci, amma ta yi gargaɗin cewa dole sai ta ƙara ƙaimi domin cim ma hakan.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 14 hours 59 minutes 49 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 41 minutes 14 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com