Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da bullar wata sabuwar kungiyar ‘yan ta’adda a jihohin Sokoto da Kebbi da ake kira Lakurawas.
Mai magana da yawun rundunar Manjo Janar Edward Buba ya ce ‘yayan wannan sabuwar kungiyar sun fito ne daga kasashen Nijar da Mali, kuma ya zuwa yanzu ba’a iya sanin manufar kungiyar ba.
Buba yace wannan sabuwar kungiyar wadda ta bullo bayan juyin mulkin da akayi a Nijar, ta haifar da matsala a yakin da ake yi da ‘yan ta’adda a iyakokin Nijar da Najeriya.
Read Also:
Buba yace dakarun kasashen 2 na ci gaba da daukar mataki domin tabbatar da tsaro a kan iyakokon yankin.
Bullar wannan kungiyar ya dada tabbatar da karuwar matsalar tsaron da ake fuskanta a yankin arewa maso yammacin Najeriya da rikicin ‘yan bindiga ya daidaita wajen hallaka jama’a da kuma raba dubban mutane da garuruwansu, abinda ya kai ga wasu samun mafaka a Jamhuriyar Nijar.
Kakakin sojin ya ce a watan da ya gabata, dakarun Najeriya sun hallaka ‘yan ta’adda 163 tare da kama wasu 82 da kuma kubutar da akalla mutane 80 da akayi garkuwa da su.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 19 hours 7 minutes 56 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 20 hours 49 minutes 21 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com