Home General Hauhawar farashi a Najeriya ta koma 24.48 a sabon tsari – NBS

Hauhawar farashi a Najeriya ta koma 24.48 a sabon tsari – NBS

Hukumar ƙididdiga ta ƙasa a Najeriya ta ce alƙaluman hauhawar farashi sun koma 24.48 cikin 100 a watan Janairun da ya gabata.

Wannan ne karon farko da National Bureau of Statistics (NBS) da fitar da rahoton bisa sabon tsarin tattara alƙaluma da ta fara amfani da shi, abin da ke nufin da wuya a iya a iya gane haƙiƙanin raguwa ko hauhawa a yanzu.

Alƙaluman sun nuna cewa hauhawar farashin kayan abinci ta kai 26.08 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

Kafofin yaɗa labarai na Najeriya sun ruwaito shugaan hukumar, Prince Adeyemi Adeniran, na faɗa ranar Talata cewa sun sauya tsarin ne saboda “daidaita shi da irin na sauran ƙasashen duniya”.

Ya ce karo na ƙarshe da Najeriya ta sauya tsarin ƙididdigar shi ne a shekarar 2009, inda ake ƙididdige farashin kayan da aka fi amfani da su a wannan tsakanin.

Hakan na nufin yanzu za a dinga kwatanta farashin kayayyakin da aka ƙididdige daga shekarar 2024, maimakon 2009 da aka dinga amfani da ita a baya.

“A sabon tsarin, ba matso da alƙaluman kusa da halin da ake ciki kawai muka yi ba, mun kuma ƙaddamar da sabuwar hanyar tattara bayanai don inganta yadda muke adana su da kuma sahihancinsu,” in ji shi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp