Rahotanni daga Najeriya na cewa ‘yan bindiga sun yiwa wasu kauyuka biyar da suka haɗa da Unguwan Tauka, Unguwan Lalle, Sannu da zuwa, Tsauni Dodo da Dandauka, dukkansu a karkashin karamar hukumar Kachia ta jihar Kaduna dirar mikiyan ranar Alhamis.
Wani shugaban al’ummar yankin wanda ya tabbatar wa Daily Trust ta wayar tarho faruwar lamarin, ya ce ‘yan bindigar sun kuma kai farmaki a wani yankin Fulani da ke ƙauyen Kubuwo, inda suka yi awon gaba da wasu matasa makiyaya guda uku.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 6 na yamma, inda ‘yan bindigar ɗauke da makamai suka yi ta kai farmaki tare da tilasta wa mutanen kauyukan tserewa yayin da suka riƙa harbin kan mai uwa dawabi.
Ya ce ‘yan bindigar sun gudu ne daga farmakin da sojoji suka kai a dajin Kurutu-Azara, wanda ke kan iyaka da karamar hukumar Kagarko kuma suka yanke shawarar ƙaddamar da mummunan hari a kan al’ummar da abin ya shafa.
A cewarsa, ‘yan bindigar sun kona wata mota da babur guda a Unguwar Tauka a lokacin da sojojin suka dakile sace wasu mutanen kauyen a yankin.
Rundunar ‘yansandan yankin ta tabbatar da faruwar harin amma bata bayyana cewa ko harin ya yi sanadin rayuwa ko kuma jikkata ba.











