Home General Mun tarwatsa wani sansanin Boko Haram a Sambisa – Sojojin Najeriya

Mun tarwatsa wani sansanin Boko Haram a Sambisa – Sojojin Najeriya

Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta na Operation HADIN KAI (OPHK) sun kashe mayaƙan Boko Haram da dama a wani samame da suka ƙaddamar a dajin Sambisa da ke jihar Borno.

Wannan aikin, a cewar sanarwar da shalkwatar sojojin ta fitar ta ce ya gudana ne a ranar 11 ga watan Mayu, 2025, a yankin Ladin Buttu, “wurin da aka san shi da zama mafakar ’yan ta’adda” kuma rundunar sojin ta bayyana nasarar a matsayin muhimmin ci gaba a yaƙin da ake yi da ƙungiyar Boko Haram a Arewa maso gabashin ƙasar.

Hakan na zuwa ne bayan sabbin hare-haren da mayaƙan Boko Haram suka ƙaddamar kan wurare daban-daban a jihar Borno, inda matsalar rikicin Boko Haram ta fi ƙamari.

A sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na X, mataimakin daraktan hulda da jama’a na Sojojin, Kyaftin Reuben Kovangiya, ya tabbatar da cewa sojojin sun yi arangama da ’yan ta’addan cikin kazamin fada.

“Sojojin sun yi amfani da ingantattun makamai da dabaru, lamarin da ya ba su nasara wajen kashe da dama daga cikin ’yan ta’addan, yayin da wasu suka tsere da raunukan harbin bindiga.” in ji sanarwar.

An kuma ƙwato makamai da kayan yaki masu tarin yawa, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Ladin Buttu na daya daga cikin muhimman sansanonin mayaƙan Boko Haram a yankin, “inda su ke amfani da shi wajen tsara dabaru da adana kayayyaki, da ƙaddamnar da hare-hare.”

Kyaftin Kovangiya ya bayyana cewa wannan aiki ya yi daidai da umarnin sabon shugaban Hafsan Sojin Kasa na ƙara kaimi wajen kai hare-hare da rushe cibiyoyin Boko Haram a yankin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp