Home Labarai Kano Ta Zama Cibiyar Bincike da Maganin Cututtuka na Zamani — Farfesa...

Kano Ta Zama Cibiyar Bincike da Maganin Cututtuka na Zamani — Farfesa Hamisu Salihu

Darakta Janar na Cibiyar Bincike Mai Zaman Kanta a Kano (KIRCT), Farfesa Hamisu Salihu, ya bayyana cewa sabbin fasahohin zamani da aka samar a bangaren lafiya sun sanya Jihar Kano ta fara taka rawa a matsayin cibiyar da za ta rika bayar da kulawa da magani na zamani a Najeriya.

Farfesa Salihu ya bayyana hakan ne a ranar Talata, yayin wata ziyarar duba wuraren aikin cibiyar da ke Kwanar Dawaki, a karamar hukumar Dawakin Kudu. Cibiyar na dauke da na’urori na zamani da ake amfani da su wajen bincike, nazari, gano cututtuka da sauran bangarorin da ke kara habaka a fannin kiwon lafiya.

A cewarsa, tare da sabuwar na’ura mai suna Next Gen 2000, cibiyar za ta taimaka wa marasa lafiya musamman masu fama da cutar Kansar Mama wajen gano ainihin nau’in cutar da ke damunsu. Wannan zai saukaka wajen samun maganin da ya dace da kowane nau’i na cutar, abin da zai karfafa damar warkar da marasa lafiya.

“Na’urar Next Gen 2000, wadda ita ce ta farko a Arewacin Najeriya, tana iya gano kwayar halittar kowanne irin kansa (cancer). Wannan bayani zai taimaka wajen gano ainihin nau’in cutar, kuma hakan zai ba mu damar daidaita magani daidai da nau’in kwayar cutar. Wannan ci gaba ne mai matukar amfani wajen ceton rayuka,” in ji Farfesa Salihu.

Ya kara da cewa, tare da na’urori irin su MI SEQ 1100+, B2 Solo – DNA, da kuma fasahar pharmacogenomics, jihar Kano ta yi watsi da tsoffin hanyoyin kula da cututtuka, ta kuma rungumi tsarin binciken ainihin tushen cuta da samar da magani da ya dace da kowanne mutum.

“Muna fatan ganin sabbin masu ba da kulawa a bangaren lafiya daga Kano, wadanda za su bayar da kulawa ta musamman ga kowane mutum. Lokacin amfani da irin magani daya ga kowa ya wuce. Tare da fasahar pharmacogenomics, za mu iya bayar da magani bisa bukatun kowane mutum,” in ji shi.

“Mun fara rage kashe kudade a bangaren lafiya, muna kara kudaden shiga ga jihar Kano, tare da inganta tsarin kiwon lafiya a jihar da kuma kasar baki daya,”

Har ila yau, ya bayyana cewa Hukumar Kula da Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) da wasu hukumomin tarayya sun nuna sha’awarsu ga wannan cibiyar. Ana shirye-shirye don turo ma’aikatansu zuwa Kano domin koyon yadda ake amfani da fasahar genomics surveillance a kasar.

A yayin zagayen, an kuma bayyana cewa cibiyar na da asibiti na zamani da ke karbar marasa lafiya tare da basu kulawa ta musamman ta hanyar amfani da na’urori da kayan aiki na zamani.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp