Home General Najeriya na fuskantar tsaiko kan shirinta na karɓar Dala biliyan 5 daga...

Najeriya na fuskantar tsaiko kan shirinta na karɓar Dala biliyan 5 daga Saudiya

Wani rahoton Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ce ana fuskantar tsaiko a tattaunawar da ake yi tsakanin Najeriya da kamfanin man fetur mafi girma a duniya mallakin Saudiya wato Aramco, dangane da shirin karɓar rancen Dala biliyan 5 da Najeriyar za ta biya da ɗanyen manta.

Wasu majiyoyi huɗu sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa faɗuwar baya bayan nan da farashin ɗanyen mai yayi a kasuwannin duniya shi ne ya janyo tsaikon, bayan da bankunan da ake sa ran za su taimaka wajen aiwatar da yarjejeniyar suka bayyana damuwa kan sauyin farashin da aka samu.

Wasu alƙaluma dai sun nuna faɗuwar farashin ɗanyen mai nau’in Brent da kashi 20 cikin 100, inda ya koma Dala 65 daga Dala 82 a cikin watan Janairun da ya gabata, abinda ke nufin idan har ba za a fasa ƙulla yarjejeniyar karɓar rancen na Dala biliyan 5 ɗin ba, to fa dole Najeriya ta ƙara yawan gungunan ɗanyen man da za ta yi amfani da su wajen biyan bashin.

Biyu daga cikin majiyoyin da suka zanta Reuters, sun ce an fara tattaunawa kan shirin karɓar rancen ne a watan Nuwamban da ya gabata, lokacin da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gana da Yarima mai jiran gadon Sarautar  Saudiya Muhd Bin salman a yayin taron tattalin arziƙin da aka yi tsakanin Saudiyan da ƙasashen Afrika. Sai dai tun babu wani ƙarin bayani da aka taɓa bayyanawa kan neman bashin da Najeriyar ke yi, in banda yanzu da kamfanin dillancin labarai na Reuters da ya ruwaito.

Idan za a iya tunawa cikin watan Mayu, shugaba Tinubu ya nemi amincewar ‘yan Majlisar ƙasar kan buƙatar gwamnati ta karɓo bashin Dala biliyan 21 daga ƙasashen ƙetare, wanda kuma a ciki ne Najeriyar ke neman rancen na dala biliyan 5 daga kamfanin Man Saudiya na Aramco.

Ya zuwa yanzu dai kamfanin dillancin labarai na Reuters bai gano manyan bankunan da za su taimaka wajen aiwatar da wannan yarjejeniya ba, sai dai majiyoyinsa sun shaida masa cewar akwai guda daga nahiyar Afrika, yayin da ragowar za su kasance daga Yankin Gabas ta Tsakiya.

Idan har wannan yarjejeniyar karɓar bashin ta ƙullu, za ta kasance mafi girma irinta da Najeriya ta shiga, kuma karo na farko kenan da irin hulɗar ke shiga tsakanin Najeriyar da Saudiya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp