Home Labarai Ban koma jam’iyyar APC ba – Namadi Sambo

Ban koma jam’iyyar APC ba – Namadi Sambo

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Mohammed Namadi Sambo, ya ƙaryata jita-jitar da ke cewa ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC, yana mai jaddada cewa har yanzu shi mamba ne na jam’iyyar PDP.

A wata sanarwa da tsohon mai taimaka masa a harkar yaɗa labarai, Umar Sani, ya fitar, Namadi Sambo ya bayyana jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta a matsayin ƙarya mai cike da ruɗani da kuma wata don ɓatar da jama’a.

Sanarwar ta bayyana cewa hoton da ke yawo da ya tayar da wannan jita-jitar wanda ke nuna Sambo tare da gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, tsohon hoto ne da aka ɗauka shekaru da suka wuce a lokacin da gwamnan ya kai masa ziyara ta jaje a gidansa da ke Abuja, bayan rasuwar ɗan uwansa, marigayi Sani Sambo.

“Wasu na ƙoƙarin amfani da hoton domin yaudarar jama’a da ƙirƙirar labarin da bai da tushe ne kawai.” Sanarwar ta ƙara da cewa

Haka kuma, sanarwar ta jaddada cewa “halartar da Namadi Sambo zai yi wajen ƙaddamar da gadajen asibiti 300 a Kaduna a ranar 19 ga watanYunin 2025, ba ya nufin ya sauya sheƙa ko ya nuna goyon bayan siyasa ga wata jam’iyya.”

Sanarwar ta bayyana cewa shi ne ya fara aikin wannan asibiti tun a lokacin da yake ofis, kuma hakan wani ɓangare ne na gudummawarsa ga ci gaban Jihar Kaduna da hidimar jama’a.

“Babu wani yunƙuri daga Namadi na sauya sheka zuwa kowace jam’iyya,” in ji sanarwar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp