Gwamnonin arewacin Najeriya sun nuna alhinin su bisa rasuwar jagoran ɗarikar Tijjaniyya a Najeriya Shiekh Dahiru Usman Bauchi wanda ya rasu a yau alhamis.
Gwamnan jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahaya, wanda shi ne shugaban ƙungiyar ta gwamnonin jihohin arewa, ya bayyana Shehin a matsayin malamin da rayuwarsa da koyarwarsa suka taɓa rayukan miliyoyin mutane a tsawon shekaru.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnatin jihar Gombe Uba Misili ya fitar, Gwamnan ya ce Sheikh Dahiru Bauchi ya sadaukar da rayuwarsa ta tsawon shekara 100 wajen yaɗa ilimin addinin musulunci, inda ya taimaka wajen koyar da karatun al Qurani da Hadisi da fiqihu da sauran karatuka.
Shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewacin Najeriyar ya kuma ce malamin ya taka muhimiyyar rawa wajen samar da zaman lafiya,da juriya, da haɗin kai da kuma tarbiyya a tsawon rayuwarsa.
Ya kuma miƙa ta’aziyyar ɗaukacin gwamnonin arewacin Najeriya ga iyalan marigayin, da mabiya ɗariƙar Tijjaniyyah, da ma alummar musulmi kan gagarumin rashin da aka yi.












