Home DUNIYA Yaƙin Iran: Hauhawar farashin Kaya a Najeriya ya ƙaru

Yaƙin Iran: Hauhawar farashin Kaya a Najeriya ya ƙaru

Food

Yaƙin Iran: Hauhawar farashin Kaya a Najeriya ya ƙaru

 

Hauhawar farashi a Najeriya ya ƙaru sosai a watan Maris a karon farko cikin wannan shekara, kamar yadda alƙaluma daga hukumar ƙididiga ta ƙasar suka nuna.

Ana ganin lamarin zai ƙara haifar da cikas ga gwamnatin ƙasar ƙarƙashin Bola Ahmed Tinubu a daidai lokacin da ake tunkarar zaɓukan 2027 a watan Junairun baɗi.

Ƙasar wadda ta fi kowace ƙasa yawan al’umma a Afrika na ta ƙokarin rage hauhawar farashi kafin a fara yaƙin Iran, inda gwamnatin ke ta ɗaukar matakai da dama a cikin watanni 11 da suka gabata.

Sai dai yaƙin Gabas ta Tsakiya ya mayar da hannun agogo baya musamman sakamakon tashin farashin man fetur, inda ya shafi farashin kayan masarufi.

Hukumar NBS a ƙasar ta ce hauhawar farashi ta ƙaru daga 15.06% a watan Fabrairu zuwa 15.38% a watan Maris.

Hauhawar farashin kayan abinci kuma ta ƙaru daga 12.12% zuwa 14.31%

Wasu al’ummar ƙasar sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa hauhawar farashin da ake samu a Najeriya na ƙara jefa rayuwarsu cikin matsi da ƙunci.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp