Akalla fursuna 63 sun gurfana a gaban wata kotun Soji da ke tsakiya birnin Kinshasa na Jamhuriya Dimokradiyar Congo a jiya laraba inda za su fuskanci tuhuma kan zarginsu da hanu a kisan mutane 130 da kuma aikata fyade.
Wadanda ake zargin sun bayyana ne a gaban wata kotun sojoji da ke a harabar gidan kason Makala a babban birnin ƙasar Kinshasa.
Lauyoyin fursunonin sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa ana tuhumar mutanen da suke karewa da laifukan lalata gine gine da haddasa gobara da kuma ayyukan ta’addanci baya ga aikata fyade.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
A zaman da ta yi na farko a makon jiya an fuskanci rashin fahimtar juna dangane da laifuka da ake zargin mutanen da aikatawa.
A cikin daren 1 wayewar 2 ga watan satumban nan fursunoni da dama sukayi yunkurin tserewa daga gidan kaso ba tare da yin karin haske game da irin yanayin da lamarin ya afku ba.
Alkalumman wucin gadi da gwamnati ta fitar na cewa akalla mutum 129 suka mutu, 24 daga ciki an harbe su ne da bindiga, gabanin washegari mahukuntan kasar su fitar ƙarin adadin mutun biyu da suka mutu sakamakon raunukan da suka ji.
Ƙungiyar Tarayya Turai, da offishoshin jakadancin Faransa da Belguim dukanin su sun bukaci yin haske game da lamarin.












