Home Labarai An Binne Birgediya Janar Braimah da Sauran Sojojin da Boko Haram ta...

An Binne Birgediya Janar Braimah da Sauran Sojojin da Boko Haram ta Kashe

Braimah

An Binne Birgediya Janar Braimah da Sauran Sojojin da Boko Haram ta Kashe

 

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa an binne ɗaya daga cikin manyan jami’anta Birgediya Janar Omo Braimah da sauran sojojin da mayaƙan Boko Haram suka kashe a wani harin da suka kai kan sansanin soji a jihar Borno.

Braimah, wanda shi ne kwamandan ƙaramar rundunar sojin Najeriya ta 29 Join Task Force Brigade da ke aiki ƙarƙashin rundunar Operation Hadin Kai, ya rasa ransa ne a samamen da mayaƙan na Boko Haram suka kai kan sansaninsu da ke garin Benisheikh na yankin ƙaramar hukumar Kaga.

A wani saƙo da ta wallafa a shafinta na facebook, rundunar sojin Najeriya ta ce a yau Laraba 15 ga watan Afrilu ne aka binne Braimah, da kyaftin Ismail da kuma sauran sojojin da suka sadaukar da rayuwarsu a bakin aiki.

An gudanar da jana’zar ne a barikin Maimalari da ke jihar Borno, gaban iyalai da ƴan’uwan mamatan.

Cikin waɗanda suka halarci binne mamatan akwai gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum, da ministan tsaro na Najeriya Christopher Musa da babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya da kuma mutane da dama.

Najeriya na ci gaba da fuskantar ƙalubalai daga ƙungiyar Boko Haram wadda a baya-bayan nan ta ƙara ƙaimi wajen kai hare-hare kan cibiyoyin soji da kuma fararen hula a arewa maso gabashin ƙasar.

Ko a ranar Litinin ɗin wannan mako rundunar sojin ta sanar da mutuwar ɗaya daga cikin kwamandojinta yayin wani hari da mayaƙan Boko Haram suka kai kan dakarunta a ƙaramar hukumar Monguno da ke jihar ta Borno.

Boko Haram ta shafe sama da shekara 15 tana ƙaddamar da hare-hare a Najeriya, lamarin da ya yi sanadiyyar rayukan dubban mutane da raba miliyoyi da muhallansu.

Hukumomi a Najeriya na ci gaba da iƙirarin samun nasara kan ƙungiyar, sai dai har yanzu matsalar na ci gaba da haifar da asarar rayuka da dukiya.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp