Gwamnatin Tarayya ta Sauya Zarge-Zargen da ta ke yi wa Malami
Gwamnatin Tarayya ta sauya zarge-zargen da ta ke yi wa tsohon Ministan Shari’ar ƙasar Abubakar Malami, tare da ɗansa Abdul’aziz inda aka cire zargin ɗaukar nauyin ta’addanci ciki.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
A zaman kotun da aka yi a ranar Laraba, Akinlolu Kahinde wakilin hukumar farin kaya ta Naeriya DSS ne ya sanar da kotu kan sauya zargin da ake yi wa Malamin, kuma ya sa aka maye zargin da wani.
Cikin sauyin da aka samu har da cire zargin mallakar makamai.
Shu’aibu Aruwa, mai kare Malami, ya tabbatar da wanda yake karewa ya amince da cire tuhumar tare da sauya ta da wasu wanda aka karanto.
Dama tun lokacin da aka karanta masa tuhumar a baya, ya musanta zargin.
Yanzu an sake ɗage zaman kotun zuwa ranar 26 ga watan Mayu da kuma 15 ga watan Yuni domin ci gaba da saurare.












