Home Taska Duk Wanda aka Kama Yana Kasuwanci da ‘Yan Ta’adda, za a ɗauke...

Duk Wanda aka Kama Yana Kasuwanci da ‘Yan Ta’adda, za a ɗauke shi a Matsayin ɗan ta’adda – Christopher Musa

Christopher-Musa

Duk Wanda aka Kama Yana Kasuwanci da ‘Yan Ta’adda, za a ɗauke shi a Matsayin ɗan ta’adda – Christopher Musa

Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya bayyana cewa ci gaba da matsalar ta’addanci da fashi da makami a ƙasar na faruwa ne saboda goyon bayan da ’yan ta’adda ke samu daga wasu ɗaiɗaikun mutane da ke ba su abinci, bayanan sirri da kuma kuɗaɗen shiga.

Ya bayyana haka ne wajen jawabin da ya gabatar a wajen babban taron ƙasa da aka gudanar a Jihar Legas.

Ministan ya jaddada cewa akwai mutanen da ake haɗa baki da su da kuma waɗanda ke ɗaukar nauyin ’yan ta’addan a cikin al’umma, waɗanda ya ce su ne ke ci gaba da rura wutar ta’addanci a Najeriya.

Ministan ya bayyana cewa jami’an tsaro na fuskantar ƙalubale wajen kai hare-hare saboda ’yan bindigar na fakewa a cikin fararen hula.

Janar Musa ya ƙara da cewa duk wanda aka kama yana taimaka wa ’yan ta’adda ko yin kasuwanci da su, za a ɗauke shi a matsayin ɗan ta’adda.

Ya buƙaci al’umma da su gaggauta fallasa masu haddasa rikici da masu tallafa musu domin kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta addabi ƙasar, musamman Arewacin Najeriya.

Tsohon Janar ɗin sojin ya gargaɗi gwamnonin jihohi da su daina yin sulhu da ’yan ta’adda, yana mai cewa hakan ba mafita ba ce, face dabarar da ’yan bindigar ke amfani da ita wajen sake shirya kansu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Samar da Tsaro: Sojojin Najeriya sun Kama ƴan ƙasashen Wajen 46Ta'addanci: Za a Gurfanar da Mutane 400 a Gaban Kotun Tarayya da ke AbujaAn Ceto Matar Janar Rabe da ya Rasu a Hannun ƴan BindigaHauhawar Farashin Kayan Masarufi a Najeriya ya ƙaru Zuwa Kashi 15.93Rundunar Sojin Najeriya ta Gudanar da Hare-Hare Kan Maɓoyar ƴan Bindiga a Jihar KatsinaZaben 2027: NDC ta Tsayar da Ɗan Kwankwaso Mataimakin ɗan Takarar Gwamnan KanoKotu ta Umarci INEC da ta Soke Rajistar ADC Tare da Jam’iyyu 4Manyan Tsofaffin Jami'an Soji 10 da Suka Rasa Rayukansu a Hannun ƴan Ta'addaTarihin Rayuwar Janar Rabe da ya Rasu a Hannun ƴan BindigaMatsalar Tsaro: Masu Zanga-Zanga Sun Tare Babbar Hanyar AbujaDuk Wanda aka Kama Yana Kasuwanci da 'Yan Ta'adda, za a ɗauke shi a Matsayin ɗan ta’adda - Christopher MusaFarashin ɗanyen Mai ya Faɗi Bayan Amurka ta Soke Sabbin Hare-Haren kaiwa IranAmurka ta yi sulhu kan yaƙin da ta ke yi da Iran - TrumpMajalisar Wakilan Najeriya ta Amince da ƙudirin Dokar Kafa ’Yan sandan JihaHukuncin da aka Yanke wa Masu Alaƙa da Sace ɗaliban Jihar Neja
X whatsapp