Babu Dan Takara ko Tikiti da zai iya Doke Namu a Zaɓen 2027 – Kwankwaso
Jihar Kano – Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa tikitin da ya hada shi da Peter Obi ba shi da abokin hamayya wajen amincewar jama’a da kwarewa.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi 16 ga watan Agusta, 2026 a Abuja, inda ya ce hadin gwiwarsa da Obi zai iya kayar da duk wani dan takara a zaben shugaban kasa na 2027.
Jaridar Punch ta kuma ruwaito dan takarar yana mai cewa manufarsu ita ce samar da tikitin da zai hada ‘yan Najeriya ba tare da la’akari da yankinsu ko addininsu ba.
Kwankwaso ya bayyana karfinsu
Jaridar Daily Post ta wallafa cewa tsohon gwamnan Kano ya ce hadin kan nasu ya tattara goyon bayan Obi a Kudancin Najeriya da kuma tasirin siyasarsa a Arewa.
Read Also:
Ya kara da cewa wannan karfi da kowannensu ke da shi zai samar da babbar kafa ta siyasa da za ta hada al’ummar kasar baki daya.
Ya ce:
“Babu wani mutum ko tikiti da zai iya doke namu wajen amincewar jama’a, kwarewa da kuma, ba shakka, kaunar kasa.”
Kwankwaso ya kara da cewa tikitin nasu ya fi sauran ‘yan takara karfi idan aka yi la’akari da tausayin talakawan Najeriya da ke fama da matsaloli.
Ya ce:
“Ko ta fuskar tausaya wa talakawa da ke shan wahala a fadin kasar nan a yau, babu wani dan takara da zai iya yin gogayya da mu.”
Kwankwaso ya koda takararsa da Obi
Kwankwaso ya ce kwarewar da ya samu a zaben 2023 ta taimaka masa wajen fahimtar Obi sosai, lamarin da ya tabbatar masa cewa za su iya yin aiki tare.
A cewar Kwankwaso, Najeriya na bukatar sauyin siyasa saboda karuwar matsalar rashin tsaro, talauci, tabarbarewar ababen more rayuwa da kuma kalubalen da manoma ke fuskanta.
Ya ce cire tallafin man fetur bai kawo ingantuwar rayuwar ‘yan Najeriya ba, yayin da manoma ke ci gaba da fuskantar matsaloli saboda shigowar abinci daga kasashen waje cikin farashi mai sauki.












